Wacece Shazmah [Episode 3] The Mermaid Princess (Hausa Novel)

BISMILLAHI, GABATARWA
MUNA MIKA GODIYARMU GA ALLAH SWA DA
YA BAMU DAMAR KARANTA MAKU LITTAFI MAI SUNA
WACECE SHAZMAH, WANDA HAFSAT MUHAMMAD
ARABI TA RUBUTA.
A MADADIN GIDAN HAUSA NOVEL DA MUKA
DAUKI NAUHIN KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN.
SAI MUSTAPHA MUHAMMAD MUSTAPHA DAYAYI
HIDIMAR KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN MUKECEWA KU KASANCE DAMU A CIKIN LITTAFI MAI
SUNA WACECE SHAZMA.

Bisimillahi Rahamanir Rahim
 Labarine me dauke da
abubuwa da dama, Saboda kar6uwar labarin ba sai mun tsayawa bayani ba, sai dai
kunbiyo muji yadda zata kasance.
WACECE SHAZMA

DOMIN SAURAREN WANNAN LITAFIN A YOUTUBE 


PAGE 3
ke kike magana"
Tambayar ta matukar bata mamaki harta
juya ko anshigo ne ganin bakowa yasa tamaida kanta kasa,
Mairo ce ta shigo musu da abun kari
" ajiye a kasa"
Nan ta dire masu tafita tabarsu zama
yayi " zauna muyi break",
Kallon falon take da abubuwan dake
ciki duk sabbin abubuwa ne gunta hango,
Carafe idanunta suka sauka akan glass
din da kifayen ke yawo "ha uhm" abunda tafada kenan sanda ta zura da
gudu ta karasa gun glass din,
Bude gashin da ya rufe mata idanu
tayi duk suka koma baya fuskarta ya bayanna wani irin murmushi ne hannunta
takai tasa ciki taji bata kai cikin ruwan ba,
Shaheed dake kallonta mamaki ne ya
kama shi sosai yadda take lokaci guda yaga yadda kifayen ke wassani cikin ruwan
ya sauya abunda baitaba gani ba,
Tsale tayi  tana dariya da
alama suna communicating da kifayen dube2 tafara ajikin glass din amma ta rasa
gane Kansa,
Komawa tayi ta durkushe a kasa sai
kuma tafara kuka tunawa da gida da tayi,
Ganin haka yasa doctor ya tashi daga
mazaunin sa yazo gare ta sunkuye fuskarta take tana hawaye sai sheshekar
kukanta da yake ji,
" meyasa ki kuka taso muje kici
abinci"
Dagowa tayi suka hada ido tana nuna
mishi glass din.

Sam baya cikin hayyacinsa dan ya
shagalta da kallon kyawawan idanunta Wanda kusan tunda yake bai taba gani ba,
Ganin yadda yake kallonta yasa tafara
tsarguwa,
Tabo shi tayi wani irin ajiyyar
zuciya yayi " Masha Allah",
Ya fada a ransa dan a dan tsorace ya
farfado " kifayene aciki" tashi muje zanyi late ya duba agogon
hannunsa,
Bin hannunsa itama tayi da kallo
tashi yayi ya koma gun kayan break din,
Tabe baki tayi itama tabi bayansa
tashin farko foodflask din daya bude ferfesun kifine ciki,
Tsale tayi ta tashi Tana ihu tana
nuna cikin kular,
Take tafara sheka mai amai tuni ta
wanke shaheed.
"mom do you hear that"
Saal ya tambaya tare da ajiye spoon
dinsa " eh kamar ihu nakeji part din big bro"hadil tafada,
Tashi sukayi su duka suka dunguma
zuwa cikin part din shaheed inda suka tarar dasu cikin wannan yanayin,
" mairo!"
Mairo!!",
Mom ta kwalla ma mairo kira "
maza kidauke mun mahaukaciyar yarinyar nan da gani",
" ahto bro you see kai me
tausayi now look at abunda yarinyar nan taimaka yanzu mtsw"
Saal yafada tare da barin part din,
" hmm wae ma Ina bro kaganta I
can't stand here ma walh jifa" hadil ma tayi nata hanyar.

Dad kam baice komai ya juya abunsa
nan shaheed yatashi yaje yayi wanka ya shirya,
Tuni sauran yan uwansa sunkama hanyar
su sai momy ya tarar a falo tana kallo,
" shaheed wai Ina kasamo wannan
yarinyar",
" a daji naganta"
" dame" tafada tana fada
kirji lallai lallai duk yadda zakai kasan yadda zakai dan badai a gidan nan ba
ba zan lamunta ba sam",
" Insha Allahu zansan abunyi but
just let her stay just for days kafin nasan abunyi",
Badan taso ba ta amsa ya mata sallama
a kofar sa ta fita yaci karo da khary,
" bro Ina zuwa da sauri
haka"
Kallonta yayi ya dauke kai batare da
ya kula ta ba yabar gidan " hmm indai nice zaka zo kasameni".

" oyoyo"
Tafada tare da dan Kara gudunta zuwa
gun mom wacce ke washe baki,
" diyar Albarka welcome but hope
kin hadu da mutumin naki yanzun nan ya fita",
Murmushi khairy tayi tare da tabe
baki " naganshi like always ba wani sauyi a tattare dashi",
" zai sauya karki damu just kici
gaba da hakuri da kuma kokarin janyo hankalinshi in no time zaki same shi balle
get up",
Mom tafada tare da mata alamun ta
tashi,
" dan jujjuya naganki"
Jujuyawa tayi " Masha Allah dawo
kizauna ba namijin da zai ganki baison ba rabu dashi a hankali",
Riga da Wando ne jikinta Wanda sun
bala'in matse mata jiki sai dan mayafi da baiko sauka kafada ba tana da diri
dakyau ba laifi ba za'a kirata baka ba bakuma za'a kirata fara ba,
Tana da kyau sosai irin hakan yasa
take abunda taga dama Uwa uba ga kudi fa iyayen ta kedashi.
" mairo kizo kiba ta abunsha
maza"
Fitowa mairo tayi dauke da tsintsiya
daga part din shaheed da Parker Wanda amai ne a ciki,
Tazo gab dasu zata wuce  tabe baki
khairy tayi,
" york what the hell is this"
Murmushi mairo tayi " amai"
da gayya tafadi mata nan khairy tafara toshe hanci Tana kakkari,
" oya wuce mana"
Dariya mairo tayi ta wuce " uwar
tambaya zanyi maganinki".

" mom meye wannan bro bashi da
lafiya ne yake amai"
Tabe baki mom tayi " kedae bari
kawai labarin bamai dadin ji bane anjima nafada miki dan yanzu takaici abun
kebani",
" ga shi"
Mairo tafada sanda take ajiye tray gaban khairy,
" no ki dauke bazan iya cin
komai yau a hannunki ba dan haka ki kwashe kazantarki kibace mun dagani",
Haka mairo ta kwashe ta mayar taci
gaba da ayukanta tabarsu suna hirarraki Wanda da yawa bai wuce yadda za'a shawo
kan shaheed ya sota ba,
A karshe ma da aka gama gyaran part
din shaheed nan tace ma mom zata ta kwanta,
Mom bata musa mata ba tawuce abunta
tasa ma kofar key,
Nan tayi bincike2 dinta tagama karshe takoma kallo.

Shiga company din yayi cikin takama
da isa ana gaggaida shi ma'aikatan wasu ya amsa wasu ya share,
Bayan ya shiga office dinshi ya zauna ne ya danna dan bell din,
Ba'ayi 1mins ba wata kyakyawar fuska
ta bayyana a office din,
" sir good morning I am Sofie
your new secretary" tafada tare da mika mai hannu,
Gani tayi gaba daya idannunsa nakanta
especially boobs dinta da suka dan showing a saman suit dinta,
Saboda bata sa babban mayafi ba ganin
kallon da yake yasa tasa hannu tadan Kara budewa,
Tare da matsawa dasu saitin fuskarshi
gab da gab tasa hannu ta tabashi " Sir"
Wani ajiyar zuciya yayi murmushi tayi
tadan yi baya,
Ganin tana murmushi yasa yace "
who are you",
Murmushi tayi tare da dan gyara
tsayuwa yadda jikinta zai kada tace " I am your new secratery",
"Wow"
Yafada ganin irin kallon da tamai
yasa yayi gyaran murya " I mean welcome what's your name",
A hankali cikin siriryar voice dinta
tace " sofie"
Sosai sunan yadan duke shi kuma ya
kalla fuskarta tabbas sunan ya face da kyanta,
" you call sir do you need
anything"
Ta katse mishi tunani " no Zaki
iya tafiya",
Juyawa tayi a hankali yadda take
walking sosai heart dinshi ke beating saboda bombom dinta dake kada was suke
juyi harta fice rufe eyes dinsa yayi,
" Sofie"
Ya fada a hankali sai yayi murmushi
ya ciza lebensa tare da jifa da dan pen din dake hannunsa yana juyi a kujerar.

Doctor shaheed yau tunda yaje office
yake tunanin yarinyar daya tsinta dan yakasa fahimtar komai a kanta,
" doctor we have emergency"
Nurse din tafada sanda tashigo office
dinshi,
" is doctor khamis not around
dan yau bana Jin zan iya wani abu"
" are you ok"
Ta tambayeshi saboda yanayin da yake
ciki kamar akwai damuwa a fuskarshi,
" no maryam but please kinema
wani daga doctor yayi handling please",
"Ok Sir"
Haka tafada ta fita dan tasan baya
taba cemata ta nema wani inda lafiyarsa kalau,
" I know just like that bazai
looking haka ba",
Taba ta akayi ta baya " yau make
faruwa maryam naga kina magana da kanki and you look worried",
Murmushi maryam tayi " bakomai
kawae normal life things kingane ae",
Tana kaiwa nan ta wuce dan kiran doctor.

See you in our next page
Wacece Shazmah [Episode 3] The Mermaid Princess (Hausa Novel) Wacece Shazmah [Episode 3] The Mermaid Princess (Hausa Novel) Reviewed by Gidan Hausa Novel on 10:03:00 AM Rating: 5

No comments:

Thanks

Popular Posts

Powered by Blogger.