Wacece Shazmah [Episode 4] The Mermaid Princess (Hausa Novel) July/03/2020

BISMILLAHI, GABATARWA
MUNA MIKA GODIYARMU GA ALLAH SWA DA
YA BAMU DAMAR KARANTA MAKU LITTAFI MAI SUNA
WACECE SHAZMAH, WANDA HAFSAT MUHAMMAD
ARABI TA RUBUTA.
A MADADIN GIDAN HAUSA NOVEL DA MUKA
DAUKI NAUHIN KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN.
SAI MUSTAPHA MUHAMMAD MUSTAPHA DAYAYI
HIDIMAR KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN MUKECEWA KU KASANCE DAMU A CIKIN LITTAFI MAI
SUNA WACECE SHAZMA.

Bisimillahi Rahamanir Rahim
 Labarine me dauke da
abubuwa da dama, Saboda kar6uwar labarin ba sai mun tsayawa bayani ba, sai dai
kunbiyo muji yadda zata kasance.
WACECE SHAZMA
DOMIN SAURAREN WANNAN LITAFIN A
YOUTUBE



PAGE 4
MASARAUTAR MAISUM
" Omid inajin tsoron hukuncin da
sarauniya zata dauka inta gano cewan SHAZMAH ta kubuta daga tsoron data
mata",
"Sabeer ya zanyi duk cikin
masarautar nan ba inda bansa a nemo ba lungu da sako amma Sam ba labarin
SHAZMAH",
Shiru su duka sukai kowa da abunda
yake sakawa a zuciyarsa,
" amma kaduba gidan mahira
kuwa"
Girgiza kai Omid yayi " inaso na
duba amma hakan zaisa sugano SHAZMAH bata nan,
" yin hakan kuma kasan mezai
jawo ga wannan masarauta",
" Hakane kuma kana da gaskiya
amma kayi kaffa2 kar gimbiya tagano kadan idan sahima ta gano kamar maman mu
tajine",
Mamakine sosai a fuskar Omid yadda
sabeer yafita daban akan mahaifiyar sa gimbiya safwana da kanwarsa sahima,
" karka damu zanyi iya kokarina
na tabbatar gimbiya bata sama labarin batan SHAZMAH ba,
" ba mamaki ta buya cikin gogo
duk inda tayi kwana daya nasan zata fara kokarin dawowa itama dakanta",
Dafa kafadarsa sabeer yayi "
Toni  zan koma ciki saina fito",
Sosai yaji dadin tattaunawarsu da
sabeer sai dai yana tsoron yadda zai kubuta daga azabar gimbiya duk sanda
labari ya iske mata.

" umma meyasa kika hanaki zuwa
ga SHAZMAH a wannan lokaci da zata fi bukata ta",
Murmushi mahira tayi " sanin
kanka ne yadda nakeson shazmah kamar ni na haifeta haka nakeji ko",
Gyara zama yayi " hakane amma
umma meye dalilinki",
" koka sama labarin masu gadin
gidan sarauta na bincike kuma anrasa gane me suke nema",
Shiru yayi kafin yace " tabbas
nasamu dan na hadu da Omid amma bai ce mun komai ba",
" kafi kowa sanin some suke nema
SHAZMAH suke nema da alama basu so sarauniya ta gano suna tsoro",
" to umma mezai shafi tafiyata
da wannan",
Murmushi tayi me sauti " lallai
yaro yarone " to kasani yanzu duk motsinka a idanunsu yake kana barin nan
zasu San daga gurinmu ne basai nafada maka abunda safwana zatai mana Ko bayan
tafiyarka ba,
" ba kaina nakeji ba sai yar
uwarka",
Ajiyar zuciya maalik yayi tabbas
yasan Tana da gaskiya hakan yasa yace " toshikenan zan cigaba da jiran
sanda zakimin umarni amma inaso kiban iznin bayansa gun SHAZMAH koda zata
bukaci hakan",
Ba'a son ranta ba amma tasan maalik
bazai iya rayuwa ba tare da SHAZMAH ba tun suna yara hakan yasa ta amince
mishi.

Zaune take tana sheka dariya gefe
kuma wani katon bawane tasa yake ta zabgar wata budurwa,
" dadina dake gimbiya sahima
baki wasa da bayi Sam",
" Aisar meye amfanin bawa yanzu
ba gashi suna shagaltamu da wannan ihun nata ba hahahahaha",
Itama Aisar din dariya tayi " ya
kinga mutumin ki kuwa"
Gyara zama sahima tayi,
" nayi kwana biyu banga maalik
ba kinman tuna mun yakamata naje naganshi dan,
" tunda sarauniya ta tsare
wannan shegiyar yarinyar daya nace ma banjeba",
Bude baki Aisar tayi cike da mamaki
" yanzu kina nufin baki ganshi ba tun lokacin"
Daga kai sahima tayi " eh
mana",
" to kiyi kokari yanzu ne
lokacin da Zaki ja hankalinsa zuwa gunki",
Murmushi sahima tayi " hakane
kuma muje kitayani na gyara muje kash wannan mamar tasa banso mahira",
Dariya Aisar ta kama,
" meya baki dariya",
" ki gafarceni gimbiya ta amma
wannan ae ba matsala bace indai shi din yana sonki dole ta ajiye kayan yakinta
tabi",
" hakane"
Nan suka cigaba da hirarsu inda
GUNSU SHAZMAH
Yamma tayi lis inda SHAZMAH ta gano
zata iya magana dasu Tana gane komai nasu,
Kwance take mairo na bata labarin
halayyar 'yan gidan kamar ance tashi ta tashi zaune,
Daga hannunta tayi kamar jiya haske
yabi ta dakatar da mairo wacce keta zuba kamar kyan ya,
Bango ta kallah inda take khairy ta
bayyana a bango tana zuba abu a cikin abinci,
Harta gama ta juya SHAZMAH na ganinta
inda SHAZMAH ta mika hannu foodflask din ya bayyana a gabanta,
Metayi naga wani abu yashiga ciki
komai ya bace har foodflask din komawa tayi ta kwnata abunta,
Juyawa tayi ta kalla mairo "
surutu" tafada ta girgiza kai kamar batason sakinta sai kuma ta tashi
saketa tare da goge komai,
" mema nake fada miki kinga
wannan khairy din Sam ba mutuniyar kirki bace",
Shiru tayi kuma Tana kallon SHAZMAH
dake kwance,
" wai ke daga Inakike ban taba
ganin mutum me kyan ki ba amma ba kasar nan kike ba",
Shiru SHAZMAH ta mata ganin bata da
niyyar bata amsa mairo tafara Jin haushi,
" tun tuni inata baki labari kin
wani shareni kina kallonki",
" eh bansan me zance miki
ba"
Zaro ido mairo tayi " kambu ke
kikai magana",
Sosai muryar ta duke mairo " dan
Allah kikuma yin magana naji",
Juyowa SHAZMAH tayi dan wannan sabon
kalma ce cikin yaren da ta samu na bil'adama,
Kallon mairo tayi amma maimakon ta
tambayeta saita barshi akan zata tambaya bagur dinta.

Komawa daki khairy tayi cike da
nishadi ganin tayi abunda takeso wayar ta ta dauka,
Ringing biyu aka dauka " hello
friend" dake speaker tasa " shegiyar gari ya akayi",
Aka bata amsa daga daya bangaren,
" hmm kedai bari aikin nan dai
yau natabbatar na zuba inagidansu doctor",
Dariya sukayi su duka " gaskiya
ne kawata baki da sauki shiyasa kike burgeni",
" kedai bari haka kawae da na
tsaya inata wahala da sunan yasoni bayan akwai hanyoyi da za'a yi komai ta
karfi",
Dariya ta cikin wayar tayi "
hakane kam yanzu dai ba garam-garam ba tai mai",
" ae Insha Allahu nasan ya kusa
dawowa komai zai zo mana da sauki zankiraki kiji ya muka karke",
" I trust you walh kawata",
Nan sukai sallama ta ajiye turo kofar
dakin akayi she is very shocked tsayawa tayi cak,
Tana wurga idanu  kamar mara
gaskiya kallonta yake da angry face dinshi,
Nuna ta yayi da yatsa " ke meya
kawo ki dakina bana fada miki kifita daga cikin duk wani abu mallakina
ba",
Kasa magana tayi ta tsaya cak agun
Tana rarraba ido dan Sam bai mata wasa,
" ba magana nake dake ba",
Jiki na bari batare da ta bashi amsa
ba tabi ta gefe da gudu tayi kofa tabar part din,
Girgiza kai yayi ya ajiye yar jakar
da ke hannunshi yabi bayanta,
" mom! Mom!! Mom!!!"
Fitowa tayi da sauri a tunanin ta
wani mugun abu ne ya faru,
" doctor kadawo lafiya why are
you shouting my name iye",
Banda ajiyar zuciya ba abunda yake
cike da bacin rae ya bude baki,
" mom nasha fada miki kidaina
barin wannan yarinyar Tana shiga premises dina amma Sam anji why",
Tsaki tayi " yanzu shaheed
saboda yar uwarka kake wannan hawa da saukan na zuciya dan kawai tashiga part
dinka iye".

" Ah mom let be fair dan Allah
why will she keep bordering him is he a kid da za'ace baisan abunda yakeso
ba",
Saal daya shigo lokacin Yafada
hararshi tayi " kai kuma waya sakoka ciki tashiga din",
Saidai shaheed juyawa yayi yakoma
dakinsa,
Inda yayi wanka yasa jallabiyarsa
doguwa yafito,
" mairo!"
Da gudu tafito kitchen din ta amsa,
" Ina yarinyar nan taci abinci"
Murmushi mairo tayi " dakyar ta
yarda amma taci sosai fa har saida nayi mamaki",
"Ok nagode mairo kikawo mun ita
garden kafin natafi masallaci",
Da sauri tabar gun tana " yanzu
ma kuwa",
Shikuma ya wuce mom da khairy dake
falo na kallonshi ba Wanda ya tanka,
" hmm banma baki labarin ba
dazu" mom tafada tana kallon khairy,
" ae hadil taban labari
dazu" bata rae mom tayi,
" karki damu yan kwanaki nayarda
tayi datayi zata bace mana gida"
" aikuwa kunyi ma kokari wai Ina
ma hadil dinne",
Khairy ta tamabaya " ae bazaki
ganta yanzu ba dazu tafice wae suna da party birthday din kawar ta kinga ko sai
anganta",
Nan sukaci gaba hirarsu.
     To be countinue👌
Wacece Shazmah [Episode 4] The Mermaid Princess (Hausa Novel) July/03/2020 Wacece Shazmah [Episode 4] The Mermaid Princess (Hausa Novel) July/03/2020 Reviewed by Gidan Hausa Novel on 12:22:00 AM Rating: 5

No comments:

Thanks

Popular Posts

Powered by Blogger.