KAINE SIRRI NA PAGE 1
KAINE SIRRI NA
PAGE 1
Sakamakon jin danayi anyi littafi maisuna "RA'AYINA"
yasa na chanza na maidashi "KAINE SIRRI NA".
Ahankali nake tafiya cikin wani babban wuri wanda aka radama
suna THE ATTORNEY 'S WORLD.
Office din lawyoyi ne sunfi dari aciki,an kawata su da
fulawowi da wasu irin madubai da wutan lantarki masu kyau daban shaawa, koni ma
shakur na shigo wurin ne Dan neman lawyer dazan bude company a wurin shi.
Tafiya na cigaba dayi harna kai gaban wani office sai naji
ana hayaniya, dariya, nadanyi nace nafasa bude kampanin dole na daukoma
matsoyana wannan rahoto.
www.naijaoutlaws.com
Bismillahi Rahmanir Raheem
"RA'AYINA ne MUZZAMIL bazan auri wacce batai graduating
ba, bazan auri under graduate ha !, nafison na auri wacce ta gama school,ta
waye, duk inda zan shiga zan iya zuwa da ita batare dajin ko dardar araina ba.
"da sauri dayan ya tari numfashin shi
yace" haba miyasa kake da tsatsauran RA'AYI ?
Kaga niko Kullum burina na auri yar sacandari, wacce zan
koyamata komi soyayya, girmamawa, biyayya, tsorona everything, duk yanda naso
tayi zatayi, zan rinka wasa ta na tankwara ta zuwa kowani position danaga dama,
kai miyasa ka banbanta da sauran mutane?
"Dan murmushi yayi yace (ra’ayina kenan) daukan keys
din motarshi dake kan table yayi ya dago yana gyara buturan gaban rigan shi
daya bude idanunshi nakan bituran dayake makalawa yace
"dama na shigo ne nafada ma gobe zan shiga MINNA(niger
state) akwai wasu case danakeda shi akasa, 3 days zanyi in sha Allah".
Muzammil yadan zaro
ido yace "garin da akai EARTHQUAKE (girgizan kasa) jiya ne zaka? "
Yakarasa maganar yana
kallon B dake kokarin makala neck tie dinshi batare da wani damuwa akan
fuskarshiba.
Muzammil yace "badakai nake magana ba, EARTHQUAKE akayi
fa koyau saida nakaranta a news, kuma daga site din da basa sa karya wato (Vanguard
news).
" B ya dafe kanshi murya chan kasa yace
"God!" Dago kanshi yayi ya kalli Muzammil yace "will you just
listen to me, ba EARTHQUAKE akayiba, Wani babban ginin bene ne ya rushe mutane
5 sun mutu Allah ya jikansu, Gobe nidai zanje nai abunda yakaini"
Muzammil yaraka shi
har wurin mota, shiga motar yayi ya zauna zaro taba kwara daya yay ya makala a
bakinshi, lighter ya dauko zai kunna yaji an fizge taban Muzammil yace
"Allah nakusa fadama mum kanashan taba,kasan baida kyau
amma kaitayi niba gashi nadena ba amma kai kaki"...
www.naijaoutlaws.com
B na ganin zai
batamai rai yaja motan yay gaba batare daya ce mai komiba.
Su uku aka zakulo daga ginin daya rushe ayau ranan jumma'a,
inda jiya aka samo biyar matattu,wurin gabaki daya bama ka iya ganin kona kusa
dakai saboda kura dake tashi,sai kukan mutane kakeji wayanda yan uwansu suka
mutu sakamakon rushewan da gidan benen yayi.
Daya daga cikin Daktan da gwamnati ya kawo wurin dan bama
wayanda sukaji rauni taimakon gaggawa,
Duba mutane ukun yayi wanda da alamu baba Mata da yarsu ne,
ya dago ya kalli sauran yan uwanshi dasuka zageyeshi cikin rashin kuzari yace
"parent din are already dead
yarinyar kuma ta bugu but tanadai rai, yanzu ai informing government mutane 7
suka mutu, wayanda suka samu injury 35 hade da yarinyar nan".
Wani irin ihu yarinyar tasaki ta zabura tafado daga gadon,
wurin iyayen nata tayi tana kuka sosai babu wanda yahanata zuwa inda suke,
tsayawa tayi tana kallonsu idanunta sunyija sosai, tai shiru ganin haka likitan
yabada umarni a wuce dasu asibiti inda ake ijiye gawawwaki idan aka nemo yan
uwansu sai abasu suje su burne.
Itakuma aka daurata
kan gado ganin yanda jikinta ke rawa, aka bata magani sanan suka cigaba da duba
sauran wayanda sukaji ciwo.
www.naijaoutlaws.com
saukowa tayi daga gado batare da kowa ya lura da itaba
tafita daga barandan da gudu.
Gudu take iya karfinta tana share hawaye bata ganin na
gabanta bata ganin na bayanta ita tadaisan tana daga kafa tana gudu iska na
kadata kwakwalwar ta abu daya kawai take hango Mata lokacin da suke kan dining
suna breakfast da Abba da Umma da ita, sai sukaji Kara sukaji ginin na rawa ji
tayi Abban ya janyota ya turata cikin jikinshi ya daura bayanshi kan nata
daganan saitaji jikin Abba yay Kara kaman ballewan kashi, ahankali ya furta
laa'ilaha illallah, tadaiji nauyi sosai ajikinta takumaji abu nabin jikinta
kaman ruwa, ihu ta dingayi tana neman taimako tana kiran umma harta sume.
Saikuma yanzu data farfado taji Abba da Umma sun mutu .
Kara gudu tayi na bala'i hawaye na tsiyaya daga idanunta
Abba maisa baka bari ginin yafadomin ba nima dukanmu mu mutu tare Maisa?
Kummmm kakeji tabugu dawani gini block tafadi a wurin
sumammiya jini nafita daga goshinta.
KAINE SIRRI NA PAGE 2
KAINE SIRRI NA PAGE 2
www.naijaoutlaws.com
KAINE SIRRI NA PAGE 1
Reviewed by NAIJAOUTLAWS
on
7:44:00 AM
Rating:
No comments:
Thanks