KAINE SIRRI NA PAGE 2
PAGE 2
WASHE GARI
11 na safiya tamai cikin garin Minna ahankali yake Jan
motarshi ganin yakusa kaiwa inda zaije.
dan gajeren tsaki yaja awahale "mtswww" ya
paka motar a gefen hanya, juyowa baya yay ya mika hannunshi yadauko goran ruwan
polar water dake back seat, sanan yay amfani da dayan hannun ya bude motar
yafita yafara waige-waige, wurin shiru babu mutane dayawa sai kwarori dake
wucewa, tafiya kadan yayi ya shiga wata yar karaman hanya haka jikin wani dan
gini inda yaga babu mai wucewa ya tsaya yay abunda zaiyi ya maida zip yaja
sanan ya juyo zai koma wurin motarshi yaji alumun numfashin mutum, cigaba da
tafiya yayi dan atunaninshi wani naman daji ne, kaman ance ya kalli kasan wurin
saiya ga jini, tracing dige digen jinin ya dinga bi haryakai bakin wani gini da anfara ba'a karasa ba, tsayawa
yayi shi bai shiga ba shikuma bai juyaba waigawa ko ina yayi yaga babu kowa awurin
yakara kallon kasan yadaiga ga jinin da alamun koma wanene yana cikin ginin,
bismillah yayi ya shiga kai tsaye yafarabin sahun jinin harya kai bangon
karshe, ganin mutum yay akwance shame shame baya ganin fuskan daga inda yake
saidai yaga zanin atampa ajikinta, karasa wa yayi ya tsugunna gabanta yana
kallonta sama da kasa, numfashi yaji tanayi ahankali awahale hakan yasa yakai hannu ya juyo da ita yana
mai karema fuskan ta kallo "Subhanallah" ya furta ganin yanda
goshinta ke fitar da jini da sauri yasa hanunshi a aljihun wandon shi handki
yaciro yadaura akan goshi yafara kallon ko ina ko akwai any clue dazai gane
daga ina take Kokuma yan uwanta, ko waya kowani abu, dawo da idonshi kanta yayi
jin tafara numfashin tana fito da harshe hakan yasa yagane ruwa takeso rike
kanta yay yadau ruwan yana bata ahankali ta shanye tass sanan jikinta gabaki
daya ya saki a hanunshi da sauri ya dagata yafito da ita daga wurin har bakin
titi yasata cikin motarshi sanan yaja da sauri dan nemamata lpy, agaban wani
babban hotel yay horn aka bude ya shiga ciki yay parking a wurin paka motoci
wasu mutane uku dukansu maza kowananen su rike da wata yar karaman littafi a
hannu suka budemai motan da sauri daya
daga cikinsu yace
"is already 12:PM, and case din damuke dashi 12:10 za'a
shiga" Fuzar da iska yayi ya dafe kanshi batare dayace komiba, daya daga
cikinsu yace " your breakfast is ready " da sauri na ukun yace "
you have visitors sir" gajeren tsaki yasaki yay gaba, sai kuma yajuyo
akasalance yace " akawai yarinya a mota, Johnson take her inside,and u
Solomon ka kira Dr ya dubata" yajuya
yahau bene, dakin da aka tanada mussamman saboda duk lokacin daya sauka
ya shiga direct bayi yaje yay wanka ya chanza kaya suwa suit baki da wandon shi
sai takalmin min baki cover mai sheki, ya cire tabaran idonshi da ruwan wanka
ya tsalla akanshi ya goge ya mayar, ya fesa designers turare mai suna kingdoms ya mike tsaye ya daura necktie sanan
yafito daga dakin.
dakin dake kusa da nashi ya shiga yaga Dr Faruk yana dubata,
kallon agogon hanunshi yayi sanan ya kalli Dr Faruk yace "am late, anjima
I will see yhu" ya bude kofa yasakai yafita saikuma ya juyo kallon fuskan
yarinyar yayi nadan tsawon sakonni sanan yasakai yafita daga dakin P.A na
binshi abaya da jakan laptop dawasu takardu a hanunshi.
www.naijaoutlaws.com
KAINE SIRRI NA PAGE 2
Reviewed by NAIJAOUTLAWS
on
9:04:00 AM
Rating:
No comments:
Thanks