Wacece Shazmah [Episode 2] The Mermaid Princess (Hausa Novel)

BISMILLAHI, GABATARWA
MUNA MIKA GODIYARMU GA ALLAH SWA DA
YA BAMU DAMAR KARANTA MAKU LITTAFI MAI SUNA
WACECE SHAZMAH, WANDA HAFSAT MUHAMMAD
ARABI TA RUBUTA.
A MADADIN GIDAN HAUSA NOVEL DA MUKA
DAUKI NAUHIN KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN.
SAI MUSTAPHA MUHAMMAD MUSTAPHA DAYAYI
HIDIMAR KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN MUKECEWA KU KASANCE DAMU A CIKIN LITTAFI MAI
SUNA WACECE SHAZMA.

Bisimillahi Rahamanir Rahim
 Labarine me dauke da
abubuwa da dama, Saboda kar6uwar labarin ba sai mun tsayawa bayani ba, sai dai
kunbiyo muji yadda zata kasance.
WACECE SHAZMA
DOMIN SAURAREN WANNAN LITAFIN A YOUTUBE
 

PAGE 2
Tunda shaheed ya taimaka suka dawo da
ita dakin mairo take kalle2,
" jeki hada mata ruwan
wanka"
"Toh",
Mairo tace tana kallon ikon Allah
tashige toilet din tabarsu nan,
" kina Jin Hausa"
Kallonsa take kawae tana kallon
kafafunsa kai hannunta tayi tana taba kafarsa data gani cikin safa,
Tana kallon kafarta Tana kallon nasa
mamakine ya cika SHAZMAH yadda KAFAR sa Tayi baki ga yatsu nasa kuma baki,
Kara kai hannunta tayi wannan karon
kokarin cire mai safa take,
"Uhm! Uhm! Uhmm!!!"
Dakarfinta ganin takasa cirewa yasa ta fashe mai da kuka,
Mamakine ya cikasa agun ya rage
tsayinsa zuwa inda zai iya ganinta " do you speak English",
Yakara dankara mata tambaya nan ma
still shiru ganin ma ya rage tsawo tana iya ganinsa yasa tajanye daga gunsa,
Mamakin gashin kanta yake yadda suka
dawo suka rufe mata fuska gaba daya haka kawae yaji yana son ganin idonta,
Hannunsa yakai a hankali Tana
"uhm uhm" tana dan ja da baya ya buda ta tamke su sosai,
Murmushi yayi me sauti Jin sautin
murmushinsa yasa SHAZMAH bude idanunta da sukai dau kamar na mage ga wani haske
da suke da sauri ya razana ya sake gashin yatashi,
Lokacin mairo tafito " baka tafi
ba" murmushi yayi
" gudnight" Yafada yayi
gaba tare da ja masu kofa.

" uhm ni dai kawae anbarni da
aiki ko daga Ina ya dibo wannan mahaukaciyar oho,
" dan allah Malama taso muje
kiyi wanka haka kawae mutum na baccinsa an wani tashe sa saboda mugunta
mtsw",
Ganin SHAZMAH Sam bata da niyyar
motsi ko alamun taa jita yasa ta tashi taje ta fincike ta
 "ahhhhhh" SHAZMAH tayi ihu,
" karki kuskura kimun ihu taso
muje kawae"
Takara fisgota cike da jin zafi da
bacin rae SHAZMAH ta dago hannunta wani blue din haske ne ya shiga idon mairo,
"Woo...",
Mairo tayi cak ta tsaya agun bata iya
motsi ko magana sai idanunta da take juya su tana kallon SHAZMAH,
Da alama Tana so ta roketa tana Jin
jiki da tsayuwar nan SHAZMAH ta bude gashin idannunta nan wani abu kamar wuta
yafito saitin bangon,
Take wani halitta ya bayyana shiba
mermaid ba shi kuma ba kifi ba sam,
Dariya abun ya mata SHAZMAH sosai
taji takara fusata "
gimbiyata karki tsorata wadanda
kikaje dan kiyi rayuwa dasu kisama farin ciki",
A fusace take kallon halittar
"bogur ban kiraka dan wannan ba
amma haryanzu bana iya yima bil'adama magana,
" duk sanda zanyi magana sai
naji Ina ihu meya sa kuma kafafuna irin nasu yaki yayi amfani meyasa".
Dariya bogur yayi tabe baki tayi
" bogur nazama abun dariya
ko",
Hadiye dariyar tasa yayi "
 yanzu zan miki yadda Zaki iya magana sannan ki
kuma iya tafiya irin nasu",
Take ya  rufe idannunsa yana budewa akanta sai wani
haske ya lullubeta har baka iya ganinta,
Cikin lokaci Kalilan sai gata tsaye a
kan kafarta,
" murmushi tayi nagode bogur
inda wani abu zan nemeka"
"Tsaya"
Ya dakatar da ita daga datse
tattaunawar su,
" wannan ki sake ta kirike
hannunta ki goge komai data gani tattare dake dan su bil'adama Zaki iya
gogewa",
Godiya tayi ta koma ta zauna tana
sakinta mairo na kokarin gudu ta damki hannunta nan ta goge komai,
Inda mairo ta cigaba da mata ihu taja
ta zuwa gun wanka ganin ruwan sosai SHAZMAH taji tsoro saboda kar tail dinta ya
bayyana,
Dakyar ta yarda mairo ta shiga da ita
harta taba ruwa sai dai ba abunda ya faru sosai taji dadi,
Nan mairo ta wanke mata kai amma
ganin bata San meye wanka bama bakaramun mamaki abun yaba mairo ba ganin yadda
ta wurgar da zanin a gabanta ta tsaya mata tairara,
Nan dai mairo ta nununa mata amma
still har lokacin SHAZMAH bata mata magana ba harta shiryata suka kwanta.

" mairo Ina bakuwa ta kikawo ta
kan nayi breakfast na fita naganta",
Murmushi mairo tayi " owk bari
na kawota",
Tsaye yake yana kurban coffee dinshi
na sabo a balcony dinsa sanda ya hango yarinyar na kalle2,
Tsayawa yayi yana kallon yarinyar dan
bayajin ya santa wa take nema and why is she dressing that way,
Sai dai bashi da amsa kamar zai sauka
ya tambaya wa take nema sai ya hango mairo,
Inda baijin me take fada tajata zuwa
dakinta inda mamaki ya Kara rufe shi,
"My bro baban coffee"
Murmushi yayi me sauti tare da maida
dayan hannunsa cikin pocket din wandonsa,
" and what do you want this
early morning"
" my darling Saal bro"
Tafada tare da rungumo hannunsa
" no sakeni karki zubarmun da coffee dina just answer the question hadil I
know for sure you need something",
 Dariya tayi " ok ok o yes of course I
want something nasan kuma zaka bani because you are my cute brother"
Murmushi yayi " so tell me now I
am tired of this long easy"
" olright sorry some cash"
Wucewa yayi zuwa dakinsa inda take
biye dashi a baya bandir din 1k biyu ya mika mata tasa hannu ta amsa
"thank yhu muaah".

Tafada tare da yima kudin kiss tafice
da gudu girgiza Kansa yayi ya shiga shiri abunsa,
Yana kamalla wa ya sauka zuwa dinning
inda already kowa ya hallara harda dad dinsu,
" wae Ina mairo ne",
" gani hajiya"
Mairo tashigo rike da SHAZMAH da
wannan karon ke cikin riga da skirt sai dai taki sa dankwali Sam taki yadda a
taje mata kai Sam,
A baje suke har fuskarta dan ba'a iya
ganin idannunta sam,
" and who is this"
Hadil ta tambayeta tare da nunota,
" my guess"
Shaheed ya amsa tare da yima mairo
nuni data kawo mai ita dinning tayi break,
" doctor don't tell me treatment
din naka yanzu har gida kakeyinshi"
Dadynsu Alhaji Ahmad M Abdulkadir ya
tambaya cike da zolayar dan nasa,
" uhm banga abun wasaba gaskiya
amma Sam bazan ci abinci da wannan a dining ba haka kawae ka tsinto yar bamu
San ma ko ba mutum bace ma kawo kace ta zo inda muje haba",
Dariya Alhaji Ahmad zancen matar tasa
yabasa sosai,
" wait wait Niima don't tell me
dama kina da tsoro niban sani ba" Yafada yana dariya sosai tsakaninsa da
Allah.

" dad is not fair gaskiya how
can we dine with someone like her wacce bamu ma San inda tafito ba,
" and I think bro should take
her to the hospital taya mu zai kawaso mana ita nan",
Sosai shaheed ranshi ya baci tashi
yayi daga dinning din suna kallonsa sun zata ma fita zaiyi,
" mairo kikawo breakfast dina da
nata falona yanzu ke kuma muje",
SHAZMAH batai mai gardama ba tabi
bayansa da tafiyar ta kamar na tata dan kafar still ba kwari,
Zuwa sukai suka zauna a falon nasa
" Ina kwana",
Juyawa yayi yana mamakin ta inda yaji
maganar ganin daga shi sai ita ya tabbatar mai da cewan itance,
Mamakine sosai a fuskarshi wani irin
dadi muryar tamai tunda yake baitaba Jin muryar data mai dadi irin wannan ba,
Mamaki ne ya rufe SHAZMAH dan mairo
tace idan tace Ina kwana za'a ce mata lafiya ma'ana anji dadin gaisuwar ta amma
saita ga akasin hakan,
Tunani tafara yadda yake mutumin
kirki yake mata komai amma bai amsa gaisuwar ta ba saita fara tunanin ko baiji
bane,
" inakwana"
" lafiya!"
Da sauri ya amsa a dan tsorace abun
nabata mamaki matuka yadda ya amsa matan.



              Saimun hadu next page kar amanta a
dunga comments....
Wacece Shazmah [Episode 2] The Mermaid Princess (Hausa Novel) Wacece Shazmah [Episode 2] The Mermaid Princess (Hausa Novel) Reviewed by Gidan Hausa Novel on 9:54:00 AM Rating: 5

No comments:

Thanks

Popular Posts

Powered by Blogger.