Wacece Shazmah [Episode 1] The Mermaid Princess (Hausa Novel)
BISMILLAHI, GABATARWA
MUNA MIKA GODIYARMU GA ALLAH SWA DA YA BAMU DAMAR KARANTA MAKU LITTAFI MAI SUNA
WACECE SHAZMAH, WANDA HAFSAT MUHAMMAD ARABI TA RUBUTA.
A MADADIN GIDAN HAUSA NOVEL DA MUKA DAUKI NAUHIN KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN.
SAI MUSTAPHA MUHAMMAD MUSTAPHA DAYAYI HIDIMAR KAWO MAKU WANNAN LITTAFIN MUKECEWA KU KASANCE DAMU A CIKIN LITTAFI MAI SUNA WACECE SHAZMA.
Bisimillahi Rahamanir Rahim
Labarine me dauke da abubuwa da dama, Saboda kar6uwar labarin ba sai mun tsayawa bayani ba, sai dai kunbiyo muji yadda zata kasance.
WACECE SHAZMA
DOMIN SAURAREN WANNAN LITAFIN A YOUTUBE
PAGE 1
"Lafiya! Lafiya!!"
Bai amsata ba saida yaje ya sauke ta kan kujera,
" shaheed wai ba magana nake maka ba wacece wannan".
" mom please kibari na dubata tukunna zan fada miki komai",
Bai saurareta ba ya nufi stairs din dake falon yabarta tsaye,
Kukan ta yasa momyn shaheed juyawa inda ya ajiye yarinyar.
A hankali ta nufi inda yarinyar take "ke daga ina",
Ta karasa tasa hannu a hankali takai hannunta inda gashi ya rufe ma yar fuska,
Budewa tayi a hankali itakuma tuni ta tsorata ta bude idanunta ae da sauri momy ta tashi.
"Innalillahi shaheed! Shaheed!!"
Da sauri wani matashi ya fito yana "momy lafiya what is happening"
Pointing masa yarinyar nan tayi shima kallon yarinyar yayi wacce bai iya ganin fuskarta sai uban gashi.
"Momy lafiya zaku tsoratata"
" wannan ba mutum bace shaheed a inaka dauko wannan yarinyar ka kawo mana gida",
Baikula taba yakarasa gaban yarinyar yafara duddubata,
ganin ba inda taji ciwo yasa shi sakin ajiyar zuciya,
"Alhamdulillah"
Yafada tare da kallon mom dinsu wacce su duka suka zuba mishi ido.
" Saal don't tell me kaima kana tsoro"
Ya mutsa fuska saal din yayi tare da yarfe hannu,
"Haba dae God forbid saikace mace" murmushi yayi "good yanzu dae call hadil for me tadan gyara yarinyar nan",
Tafi mom tayi " Ah lallai ma badai hadil ba ba abunda zaisa ta taba wannan aljanar daka kwaso ka kawo mana walh sai dai in akira mairo tadauketa sukarata".
Bai musaba yasa aka kira mairon itama da tsoro ta iya rike yarinyar dan dai ba yadda zatai ne,
" kuje sai da safe maga yadda abubuwa zasu kasance",
" kayana bazasu mata ba"
Murmushi yayi "kidauko na hadil sannan kitabattar taci abinci ok" kaidai kai tayi, amma tafiya ta gagara wannan yarinyar,
Harya juya zai tafi, tuni su mom suka bar gun
" ta kasa tafiya"? nan ya juya yaje ya duba kafar,
Abunda yabashi mamaki baiwuce santsin kafar ba,
kamar ta jarirai ba kwari, kamar ba'a taba taka taba,
" ok help me mukaita dakinki maybe zuwa gobe musamu ta taka kafar"
nan suka kaita. amma yayi mamaki sosai ta yadda yaga kafar.
MASARAUTAR MAITUM.
" Mahira natabbatar kina ganin yadda wannan bil'adaman ya dauki gimbiya Shazmah yanzu me kikeso"
Boka yafada yana kallonta,
" Inaso kamar yadda mukaYi,
a shafe komai ta yadda sarauniya safwana bazata taba sanin inda take ba duk nacinta da nemanta".
"Angama ranki ya dadade amma",
Sai kuma yayi shiru maalik ne ya kallesa "amma me",
"Muddun mukai haka to mukanmu bazamu iy ganin ya rayuwarta take ba".
Cike da bacin rae maalik ya dubi bokan "
dole kasan yadda zakai mudunga ganin ta munajin ya take"
"Maalik!"
Mahira tafada tare d daga masa hannu,
" yakai dana nasan kai ka kai yar uwarka duniyar wajen ruwa,
duniyar bil'adama nasan kai kadai zaka iya nemo inda take ka dunga samo mana labarai kanta ba aikin boka bane wannan kai nabarwa wannan amanar",
"Na miki Alkawari mamana zanyi dukkan abubuwan dakika daurani akai
zan kula da ita zan daura ta kan hanyoyi ba bazan bari tamanta daga inda take ba"
Taji dadin kalamansa kwarae hakan yasa ta rungumeshi tare da sumbatarshi a goshi.
"Amma ka kula dan haryanzu sarauniya bata samu labari ba inta samu,
" labarin batan shazmah tabbas zata tada hankalin masarauta
mu kokarta komawa gida kar a zargemu" nan suka dawo zuwa gidansu.
MIMSQUEEN ✍
Wacece Shazmah [Episode 1] The Mermaid Princess (Hausa Novel)
Reviewed by Gidan Hausa Novel
on
12:24:00 PM
Rating:
No comments:
Thanks